Akwai wani abu da na fahimta... Mutane da yawa suna tambaya, "Ta yaya zan fara samun kuɗi ta yanar gizo?" Amma ka lura? Yawanci muna neman inda za a karɓi kuɗi, ba inda za mu ƙirƙiri ƙima ba. Da na fara koyon programming, ban fara da tunanin kuɗi ba. Na fara ne da son fahimtar yadda apps suke aiki. A hankali na fara gina ƙananan apps, ina gyara kurakurai, ina ƙara ilimi kowace rana. Yau idan ka buɗe Play Store, kusan duk app ɗin da kake amfani da shi wani mutum ne ya gina shi. Na tsaya na tambayi kaina: "Me zai hana ni ma in zama ɗaya daga cikinsu?" Wannan tambayar ce ta canza min tunani. Shi ya sa na kafa AREWA EXPAND . Burina shi ne in taimaka wa matasa su koyi ƙwarewar da za ta buɗe musu ƙofofi. Ko ka yi aiki da ita, ko ka gina naka app, ko ka koyar da wasu, wannan ilimin zai ci gaba da amfani. Ba zan ce hanya ce mai sauƙi ba. Za ka yi kuskure, za ka gyara, za ka sake gwadawa. Amma idan ka ci gaba, wata rana za ka waiwaya ka ga irin nisan da ka yi. Idan kana so...